DA DUMI-DUMIN SA: Wasu ‘yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda a Enugu.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Inyi da ke karamar hukumar Oji-River a jihar Enugu, inda suka kashe mutane biyu tare da kona ofishin.
Hamada Blog ta Ruwaito cewa lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi
Daya daga cikin mutanen biyu da aka kashe an ce dan sanda ne da ke bakin aiki lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari ofishin.
Bidiyon lamarin da Hamada Blog ta gani a yammacin Lahadin da ta gabata ya nuna wani gini da ake amfani da shi a matsayin ofishin ‘yan sanda yana ci da wuta da gawarwakin wasu matasa biyu kwance a shingen ofishin.
Muryoyin da ke bayan faifan bidiyon sun bayyana daya daga cikin gawarwakin dan sanda ne yayin da babu tabbas ko mutunen biyu dan sanda ne ko a’a. Wasu muryoyin sun bayyana mutanen biyun da lamarin ya rutsa da su ‘yan sanda ne, sai dai wani ya ce zai iya bayyana daya daga cikinsu a matsayin dan sandan da ke aiki a ofishin.
Kokarin jin martanin rundunar ‘yan sandan jihar kan lamarin bai yi nasara ba domin mai magana da yawun rundunar DSP Daniel Ndukwe bai amsa kiran da SaharaReporters ta yi masa ba ko kuma ya amsa sakon da aka aika masa.