News

MAZA KU DINGA ADALCI A TSAKANIN MATAYEN KU

Da yawa wasu mazan wannan rashin adalcin shine zai kaisu zuwa ga hanyar halaka matukar maigida bai gyara alakar sa ba.

Da yawa rashin adalcin nan shine a cikin zukatan su na ware macen so,a ware macen da kuma ba’a sonta,a ware matar da ake wulakantawa a ciki,ko kuma matar da ita yanzu ba’a yayinta andaina son ta koda kowa tana kyautatawa ,wannan rashin adalcin shine zai saka baza’a ga kyautatawan nata ba.

 

Wani rashin adalcin nasa zai sayawa daya abu,amma dayan bazai saya mata ba,ko kuma ranar girkin daya yayi cefa ne mai kyau,a sayo kaza ko nama saboda ita ana sonta,ita kuma ranar girkin dayan baza’a yi cefane mai kyau ba zadai a kawo abu, saboda rashin adalci a zuciyar sa.

 

Ko kuma a gaban daya ya nuna daya bata muhimmanci a rayuwar sa,dole ne daman an sani akwai matar da zaka fi sonta a cikin zuciyar ka,amma sai kayi kokarin ganin kana kwatatan adalci a tsakanin su.

See also  DOWNLOAD TWITTER VIDEO: 12-YEAR-OLD SHOOTS COUSIN TO DEATH

 

Wata zata aure shi bashi da komai suyi wahala tare,amma ranan da Allah ya bude masa,a wannan gabar bakowane namiji bane ke adalci,sai yaje ya auro matar wanda da arzikin sa ta gansa,don rashin adalci kuma sai ya fifita fiye da wannan matar da suka sha wahala a tare kuma,ita wannan an rufe babinta kuma ga matar jin dadi,wannan kiri_kiri ya nuna rashin adalci,yama manta da ita.

 

Da yawa wasu mazan nan marar sa adalci hakan zai kaisu zuwa ga wuta.

 

Idan kasan kai bazaka iya adalci ba kawai ka hakura da mace daya karka kara balle kazo kanayin abinda zai konaka zuwa wuta.

 

Ka kula sosai kaji tsoron haduwar ka da ubangiji ka zamu mai adalci a tsakanin matayen ka.

 

©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button