News
VIDEO: Tinubu ya dawo daga Birtaniya

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya isa Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a yammacin ranar Alhamis.
Tinubu dai ya kwashe kusan kwanaki 12 a kasar Birtaniya.
Dadewar rashinsa ya haifar da jita-jita game da lafiyarsa.
Sai dai mai magana da yawun yakin neman zabensa, Festus Keyamo, ya tabbatar da dawowar sa a wani Bidiyo da ya wallafa a Twitter.
Keyamo ya saka bidiyon yadda Tinubu ke sauka daga jirgin sama ya rubuta: “Mikiya ta sauka”.
The Eagle has landed!!! 😎😎😎 pic.twitter.com/1cLvNev0zj
— Festus Keyamo, SAN (@fkeyamo) October 6, 2022