News

Illar kazanta ga mata

A yau ina so zan yi magana a kan wata muguwar al’ada wacce ta fi yawaita a gun ‘yan uwa mata. Wannan al’ada ba wata aba ba ce illa kazanta. Hakika wannan babban al’amari ne wanda ba shi da mahadi a addinance, da al’adance da kuma dabi’ance.

 

Za ku ga ita kanta kazantar ta kasu kashi-kashi ga sunan kamar haka:

 

1. Kazama ta farko: ita ce macen da za ku ganta tsaf-tsaf a waje, wato wurin biki ko suna kowani taro wanda in ka ganta za ka rantse da Allah ita din ta san me take yi, ba za ka sha mamaki ba sai Allah ya kai ka gidanta. Wato muhallinta a nan za ka raina ta, wari, zarni, karni, gashi, tsaka, duk a gidanta amma a hakan ta gyare jikinta ta bar gidanta kaca–kaca ta tafi biki.

 

2. Kazama ta biyu: ita ce wadda har gara ta farkon tun da akalla ita ta gyara jikinta gida ne sai a hankali, to ita kuwa kazama ta biyu irinsu ne sam ko ‘yar uwarta mace ba za ta so matsawa kusa da ita ba, saboda warin da za ka ji daga na bakinta zuwa na hammatarta ga na kai. Wa iyazu billah, ‘yar uwa a nan ko mijinki ya kyamace ki, ko ya wulakantaki ba ki da bakin da za ki yi korafin hakan.

See also  Dwayne Haskins Video of an Accident Scene Death Caused by a Dump Truck

 

3. Kazama ta uku: wannan kuwa kusan tafi kowacce daga cikin ta farkon da ta biyun, dan ita waannan ban da kazantar gida da ta jiki har da ta zuciya. Don a kan kazantar har ta kashe mata zuciya, domin kuwa da ka shiga muhallinta ya zama ragowar bera, ta bari yara duk sun babbala, sun ragargaza ko ina, wani gefen ga tsa-tsa da yana ko ina, ga uban wanki da wanke-wanke ko ina. Kuma duk da haka wannan be ishi kazama ta uku ba, a’a sai yawan tsegumi da rashin son zaman gida da son jin abin da ‘yan uwa da makwabta ke ciki.

 

Jan hankali

 

Gaskiya ‘yan uwana mata akwai babban aiki a gare mu kar ma idan kin kaddara ma kanki kin fito a nau’in cikin wadancan kazaman, kin ga dai ‘yar uwa ba ke ba zama lafiya da maigidanki, haka nan ba nishadi, haka zalika duk abin da ki ka yi haka ‘yar ki za ta yi a na ta gidan, kuma idan har mijinki ya yi hakuri da na ki halin ba lallai mijin ‘yar ki ya ha?ura ba don haka tsafta tana da mahimmanci ga rayuwar diya mace a nan zan iya cewa “in kunne ya ji gangan jiki ya tsira” Allah ya ba mu ikon gyarawa amen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button