News

A rana irin ta yau Oktoba 3, 2016: MOPPAN ta kori Rahama Sadau daga Kannywood

Idan dai za a iya tunawa, ranar 2 ga Oktoba, 2016, ƙungiyar Shirya Fina-finan Hausa ta kannywood Mai Suna MOPPAN ta kori Rahama Sadau daga ma’aikatar shirya finafinai, sakamakon rashin ladabi da ta yi wanda ya saɓa da dokoki da ƙa’idojin ƙungiyar, inda aka gan Jarumar ta rungumi wani mawaƙin gambara Mai suna Classic.

 

Bayan shekara biyu da korar ta, sai Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta hannun Shugabanta, Mallam Isma’il Na’Abba Afakkallah, ranar 8 ga Janairu, 2018, ta yafe wa Rahama ba tare da wani sharaɗi ba, don ta koma cikin abokan aikinta na Kannywood.

 

Matakin da Reshen MOPPAN na Jahar Kano ya ƙalubalanta a ranar 15 ga Janairu, 2020, ta hannun Shugabanta, Mallam Kabiru Maikaba.

See also  Jaruma Saima Muhammad Tayi Aure

 

A wannan gaɓa, MOPPAN tana nanata matsayinta na farko a kan RAHAMA SADAU. Tana kuma kira ga dukkan ƙungiyoyin Kannywood da su tabbatar da bin wannan doka, al’ummar Hausawa da al’ummar ƙasashen waje, su kuma lura da cewa ƙungiyar ta nesanta kanta da rashin ɗa’ar Rahama Sadau

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button