News

An Yanke wa Wani Matashi Dan shekara 23 Hukuncin daurin watanni 6 a gidan gyaran hali

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Kano a ranar Litinin, ta yanke wa wani matashi dan shekara 23, Sadiq Miko, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar akuyar da ta kai Naira 40,000.

Miko, wanda ke zaune a Tudun Murtala Quarters Kano, an same shi da laifin sata.

Babban Alkalin Kotun, Zubairu Inuwa, ya baiwa wanda aka yanke wa laifin zabin biyan tarar Naira 30,000 bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Inuwa ya kuma umarci mai laifin da ya biya wanda ya shigar da karan kudi naira 40,000 a matsayin diyya na akuyar ko kuma ya yi zaman gidan yari na watanni tara.

See also  In Orlando, a teen boy dies after falling off a ride. Twitter's Video (kid falling off ride in Orlando)

Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Mista Ahmed Sarki ya shaida wa kotun cewa wani Isah Bello na Ranji Quarters Kano ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Gwagwarwa Kano a ranar 10 ga watan Yuli.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button