News
Wadanda suka sace wasu fitattun jaruman Nollywood guda biyu sun nemi kudin fansa har $100,000

Wadanda suka yi garkuwa da wasu fitattun jaruman fina-finan Nollywood, Cynthia Okereke da Clemson Cornel, aka Agbogidi sun nemi dala 100,000 domin a sako su.
Idan za a iya tunawa, an ba da rahoton bacewar jaruman ne bayan da ‘yan uwansu suka tabbatar da cewa ba su dawo gida daga wurin wani fim ba a Garin Ozalla, Jihar Enugu, a ranar Alhamis, 28 ga Yuli, 2022.
Sai dai a ranar Asabar, 30 ga Yuli, 2022, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria (AGN) na kasa, Emeka Rollas, ya ce masu garkuwa da mutane sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa kuma suna neman zunzurutun kudi dala 100,000.
Rollas ya kuma ce mambobin kungiyar ta jarumai suna aiki kafada da kafada da iyalan wadanda abin ya shafa da kuma jami’an tsaro don ganin an sako su lafiya.