kannywood

Shin Ko Mansura Isa Na Shirin Komawa Harkar Fina-fanai?

Jarumar kannywood Mansura Isa tana daga cikin jaruman da suka yi shura a masana’antar kannywood a cikin kankanan lokaci a sanda ta shigo masana’antar musamman saboda gwanancewar ta da rawa da iya acting da saurran abubuwan da ke burge yan kallo.

Jarumar cikin kankanin lokaci ta fara fitowa a manyan finafinai a manyan kamfanunuwan shirya finafinan Hausa, fina-finan sun hada da irin su Gurnani, jarumai, Jamila, chasis da sauran su.

A shekarar 2007 kwatsam sai jarumi Sani danja yayi wuff da ita, bayan shekaru goma sha hudu da auren sai auren ya mutu bayan Allah ya albarkacesu da samun zuri’ar yaya hudu, mace daya maza uku.

Jarumar tun kafin mutuwar auren ta tana taba daukar nauyin film har yanzu ma tana yi, wanda film din ta da ta saki baya bayannan shine Mai Suna Fanan.

See also  Za'a Rufe Dandalin TikTok A Nigeria

Wani video da jarumar ta wallafa a shafin ta na tiktok ya dauki hankula, inda ta tunawa tsofaffin masoyan ta yadda take actin da yadda ake saka su kuka a fim. Kalli Video din anan

An yi ta mata tsokaci (comment) inda wasu ke mata fatan komawa dakin mijin ta wasu na kewar film irin nasu na da, wasu ko na zaton ko film din zata dawo, yayin da wasuko yabon kyawun ta da son barkwancin ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button