Jaruma Saima Muhammad Tayi Aure

Kamar yadda aka saba jaruma Saima Muhd ma sai ji aka yi ana taya ta murnar aure da tayi a shekaran jiya wanda sai a yau abokan sana’ar ta ke wallafa hotunan ta suna taya ta murnar auren ba tare da wani cikakken bayanin wanda ta aura ko inda aka yi auren da sauran suba.
Saima muhd dai jaruma ce da ta bada gudun mawa a masana’antar Kannywood tun sama da shekaru 23 da suka wuce wanda a kiyasi an tabbbatar da babu wata mace sa’ar ta a masana’antar in ba irin su mama tambaya ba amma daukacin matan da ta tarar ko suka yi zamani tare a farkon zuwan ta kannywood din daga wadanda suka rasu sai wadan da ke dakin mazajen su suna ta bayayyafa sai kuma wadan da suka ajiye sana’ar.
Jarumar Allah ya hore mata kyawon jikin da kowa ke tankawa inda har Ibrahim mandawari tun a wancan lokacin yake mata kirari da benu bakya tsufa sai dai ki sake sabon gashi amma har kawo iyanzu jarumar tana sajewa a cikin mata da ke fitowa a yan mata a finafinai irin su Hadiza Gabon, Halima Atete, hauwa waraka, jamila nagudu da sauran su.